ABNA24 : Kamfanonin guda biyu sun ce bidiyon da Trump, ya wallafa sun sabawa ka’idojinsu game da yada labaren karya.
Shi dai Trump, ya wallafa wani faifan bidiyo ne wanda a cikin yake bayyani game da annobar cutar korona.
Bidiyon dai na nuna shugaban kasar ta Amurka, Trump, a cikin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Fox News, inda yake bayyana cewa yara sun kusan samun garkuwa game da wannan cuta.
Wanda kuma a cewar kakakin kamfanin facebook, bayannan shugaban kasar na cike da labaren karya kan cewa akwai wani rukunin mutane da basa iya harbuwa da cutar ta Covid-19.
Wannan dai shi ne karon farko da facebbok ya dauki mataki kan sakwannin Trump.
Baya ga hakan kuma kamfanin twitter ya dakatar na wani dan lokaci shafin kamfe na shugaba Trump, @TeamTrump, har sai shafin ya goge bidiyon da shugaba Trump ya wallafa.
342/